<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>466</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Masoyina yana sama,
 shi ne Yesu Ɗan Allahnmu.
 Yana sama, yana shirya
 wurin zama can dominmu,
 saboda ni, ba ni da kowa,
 ko aboki a duniyan nan.
 Ruhunsa ne ya biɗa duk
 ya koya mana aikinsa.

[V2]
 KORUS
 Masu-bi ku zo, mu bi Yesu
 Yesu shi ne makiyayi. (2x)
 Karatu: Ubanmu wanda ke cikin sama ---- (Addu'ar Ubangiji)

[V3]
 2) Ku ƴan ƙwaya ku shaida fa,
 Almasihu yana zuwa.
 Ku mutane, ku shaida
 fa Almasihu yana zuwa.
 Ku Pastoci, ku yi aniya,
 ku yi aiki da aminci.
 Ku je ku yi shaidar bishara,
 ku je ku kawo ƃatattu.
 Korus

[V4]
 Karatu: Masoyina, masoyina yana sama.
 Shi ne Ɗan Allah wanda ya rnutu.
 Sabili da zunubanmu. Ƴanuwa
 Ku duba irin ƙauna da Yesu ya yi
 domin mu zama masu ƙaunar juna

[V5]
 3) Ku matasa, ku shaida fa
 Almasihu yana zuwa.
 Ku yara ma, ku shaida fa
 Almasmu yana zuwa.
 Zumuntar mata, ku yi aniya,
 Ku yi aiki da aminci,
 Ku je ku shaida bishara,
 Ku je ku kawo ƃatattu.
 Korus

[V6]
 Karatu: Kamar yadda Yesu ya koya mana,
 ku ƴan ƙwaya, da masu shaidar bishara.
 da Pastoci, da su referan, da zumuntar mata,
 ku mutane duka, ku tashi tsaye,
 ku yi aikin Ubangiji fa, gama lokaci ya kusa,
 Yesu yana zuwa. Babu shakka zai ba kowa ladan
 aikinsa.
 Allah ya taimakemu. Amin.</lyrics>
<title>Masoyina Yana Sama LW466</title>
</song>